Na Yi Alƙawarin Zan Sayar Da Duk Abin Da Na Mallaka Idan APC Ta Baiwa Zulum Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa

Na Yi Alƙawarin Zan Sayar Da Duk Abin Da Na Mallaka Idan APC Ta Baiwa Zulum Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa

Spread the love

 303 total views,  3 views today

Na Yi Alƙawarin Zan Sayar Da Duk Abin Da Na Mallaka Idan APC Ta Baiwa Zulum Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa Domin Ya Sayi Fom, Inji Wata Matashiya A Kaduna

Daga Zaharaddeen Gandu

Wata matashiya da ke kaduna ta yi alƙawari har ga Allah, zata saida duk abinda ta mallaka, daga ciki harda iphone ɗinta domin saya wa Zulum fom ɗin takarar Shugaban Ƙasa idan har aka tsaida shi a matsayin ɗan takara, Zuma Times Hausa ta rawaito cewa, matashiyar mai suna Zainab Abubakar Bako ta bayyana cewa, “ina miƙa roƙona ga mai girma gwamnan jihar Borno Babagana Umaru Zulum, da ya taimaka ya fito takarar shugabancin ƙasar nan, saboda inada yaƙinin shi zai ƙwato ƙasar nan daga irin ƙangi na matsalar tsaron da muke ciki a yanzu insha-Allah”,

“Najeriya tana buƙatar shugaba nagartacce jajirtacce mara tsoro kamar Gwamna Zulum, wanda ya fifita damuwar talakawa da ya ke shugabanta fiye da tasa damuwar”,

“sannan ina kara kira ga shugaban jam’iyar APC Na ƙasa dama dukkan wasu masu ruwa da tsaki a jam’iyar, da su duba wannan kiranye da lissafi, hasashe na siyasa, domin muga Gwamnan jihar Borno an bashi takarar shugabancin Ƙasar nan a zaɓen 2023, duba da har ya zuwa yanzu Gwamnan bai sai fom na tsayawa takara a jiharsa”,

“idan wannan hasashe nawa ya tabbata aka tsaida Gwamna Zulum a matsayina ɗan takarar Shugaban ƙasa, nayi alƙawarin zan saida komai nawa da na mallaka, daga ciki har da iphone ɗina, domin in cikawa Gwamna Zulum ya sayi fom ɗin takarar Shugaban Ƙasar Najeriya”,

“daga ƙarshe ina yi wa ƙasata Najeriya da jiharmu kaduna da ma duniya baki ɗaya addu’a, Allah ya bamu lafiya da zaman lafiya, Ubangiji ka zaɓa mana shugabanni na gari masu kishinmu ba masu kishin aljihunsu ba”. Inji Matashiyar Zainab Abubakar Bako

Idan baku manta ba, a kwanakin baya matashiyar mai suna Zainab Abubakar Bako ta fito ta bayyana ra’ayinta da kiranye na ƙungiyoyi da su tursasa Gwamna Zulum fitowa takarar shugaban Ƙasa, tare da kira ga gwamnan jihar Barno da ya taimaka ya fito takarar shugabancin ƙasar nan a zaɓen shekarar 2023.

The post Na Yi Alƙawarin Zan Sayar Da Duk Abin Da Na Mallaka Idan APC Ta Baiwa Zulum Tikitin Takarar Shugaban Ƙasa appeared first on Hausa News.

Polls

Do You Support Killing of Deborah ?

View Results

Loading ... Loading ...

 304 total views,  4 views today

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

Average rating 0 / 5. Vote count: 0

No votes so far! Be the first to rate this post.

As you found this post useful...

Follow us on social media!

We are sorry that this post was not useful for you!

Let us improve this post!

Tell us how we can improve this post?

Swordpress - Your Impartial, Comprehensive Daily News Source We scour 1000+ sources so you don't have to. Culture, science, sports, politics, business, and more—all in a less than five-minute read.
Facebook Comments Box

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

Average rating 0 / 5. Vote count: 0

No votes so far! Be the first to rate this post.

As you found this post useful...

Follow us on social media!

We are sorry that this post was not useful for you!

Let us improve this post!

Tell us how we can improve this post?


Spread the love