Fri. Apr 12th, 2024
(Last Updated On: August 29, 2023)

Shahararren jarumin fim din Hausan nan Ali Nuhu yace, rashin amfani da ingantattun kayan aiki wajen daukar fina-finan Hausa da a kamfanin Kannywood, shine dalilin daya sa kamfanin nan na Netflix basa nuna faya-fayensu.shafin zinariya TV na wallafa

Jarumin yayi wannan kalami ne, yayin daya bayyana cikin shirin nan, na tattaunawa da jaruman Kannywood da takwarsu Hadiza Gabon ke gabatarwa.

Ali Nuhu, wanda ya kasance jarumi a masana’antar ta Kannywood kusan shekaru 25, kuma sunan shi ya game gidaje yace, sabanin takwarorinsu na kudancin ƙasar, masu shirya fina-finai a masana’antar ta Kannywood, basa amfani da kayayyakin zamani wajen daukar daukar shirye-shiryensu.

Dalilin daya sa har yanzu ba'a haskaka fina-finan Kanyywood a Netflix- Ali Nuhu
Dalilin daya sa har yanzu ba’a haskaka fina-finan Kanyywood a Netflix- Ali Nuhu

Yace, ” za a iya sanya fim din kowa a manhajar Netflix, matukar ya cika ka’idojin da ake bukata, sai kana bukatar wadanda zasu tallatawa kanfanin fim din ka, amma kuma masu tallan sunfi gane tallata fin din wadanda suke da alaka ta sannayya dasu”

Sannan a acewar shi, ” ko da (Kannywood) mun cika ka’idojin da Netflix din ke bukata, to wani hanzari ba gudu ba kuma shine, batun tawagar dake aikin shirya fim din, domin a masana’antar Nollywood, na sha aikin fim, ta yadda zaka ga duk tawagar ma’aikatan yan kasashen waje ne”

Yace, “amma hakan baya nufin cewa, Kannywood ba zata iya shirya fina-finai masu inganci ba. Banbancin kawai shine aiki tukuru da jajircewa wajen hada fina-finai kamar yadda ake yi a sauran kasashen da suka ci gaba”

Ali Nuhu yace, ya taba mika fim din shi ga kamfanin Netflix, amma sai bayan watanni Bakwai suka bashi amsa, da cewa zasu yi bitar fim din, kuma har yanzu yana jira.

Sai dai yace, sakamakon fitowar Amazon Netflix, suna kokarin la’akari da fina-finai daga Arewacin Najeriya, tun da har sun bamu damar mika fina-finan mu”

“Bani da shirin barin shirin fim, saboda shine sana’ar dana iya a duk tsawon rayuwa ta” in ji Ali Nuhu

“Na fara ne, a matsayin matashi dake yawan fitowa a matsayin masoyi, muna waka da rawa. Daga baya shekaru suka sanya na koma fitowa a matsayin Uba, ina kuma da fitowa daban-daban, tare da barin barin masu tasowa, suna daukar rawar da nake takawa a baya”

“Amma, yanzu da nake fitowa a matsayin Uba, akwai alamun karshe na zuwa kenan, amma dai bani da niyyar barin harkar fim” inji jarumi Ali Nuhu.

Yace, “yanzu shekaru na 20 kenan da yin aure, domin kwanan nan, muka yi bikin murnar cika shekaru Ashirin da yin aure da uwar gida na, dana aureta tun a shekarar 2003, gashi yanzu muna 2023”

“Duk da cewa ni musulmi ne, amma batun auren mace fiye da daya baya cikin tsari na, saboda a tunani na, idan har mutum yana zaman lafiya tsakanin shi da matarsa, kuma ya san cewa, ba zai iya adalci ba idan ya karo wata matar, ko kuma hakan ya wargaza masa tsari, to ai gwara ka ci gaba da zama da mace daya”

“Wannan shine dalilin daya sa na kwashe shekaru Ashirin da mata daya, duk da cewa musulunci ya bada damar auren mace fiya da daya”

The post Dalilin daya sa har yanzu ba’a haskaka fina-finan Kanyywood a Netflix- Ali Nuhu appeared first on kannywood.ng | Best African Hausa Music Blog, Entertainment ,News and Gossips .

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

Average rating 0 / 5. Vote count: 0

No votes so far! Be the first to rate this post.

As you found this post useful...

Follow us on social media!

We are sorry that this post was not useful for you!

Let us improve this post!

Tell us how we can improve this post?