Fri. Apr 12th, 2024
(Last Updated On: March 30, 2024)

Wace Ce ( Zainab Idris )
 
Takaitaccen Tarihin Tsohuwar Jaruma Zainab Idris
 
Zainab Idris ‘yar wasan hausa ce, ‘yar rawa da kuma furodusa ce wacce aka haifa a Jos, Jihar Filato.
Naija News ta gane da cewa an haifi shahararriyar ne a ranar 18 ga Maris, 1982 a Filato.
 
Zainab ita ce ta biyar a cikin iyalin yara goma, ‘yan mata shida hadi da maza hudu.
 
Bincike ya nuna da cewa Zainab ta yi makarantar firamaren ta ne a RCM Kabo da kuma Makarantar Sakandaren Gwamnati ta Jos don karatun firamare da sakandare.
 
Ta kuma ci gaba da karatun ta har ta karbi satifiket a kwas da ta yi a kwalejin kimiyya da fasaha ta jihar Kaduna.
 
Naija News ta ruwaito da cewa Zainab ta nuna sha’awar shiga wasan kwaikwayo a lokacin da take da karancin shekaru. A karshe ta hadu da darakta, Abbas Sadiq wanda ya gabatar da ita ga wasan kwaikwayo.
 
Zainab ta yi fitar ta na farko ne a wata shiri mai taken ‘Ikama’. Ta bi wannan tare da wani shiri mai birgewa a cikin fim din ‘Kallabi’ inda ta fito tare da Safiya Musa, Hafsat Shehu, Adam A. Zango da sauransu.
 
Zainab Idris ta kuma shirya finafinai da dama kamar; Albashi, Gwanaye, Gwamnati da sauransu.
 
Yanzu Andaina Ganin Zainab Idris Bayan Aure Da Tayi Tare Da Jarumi Abass Sadiq.

Zainab Idris Ta Amarce Ne Ranar 7 Ga Watan Maris Shekara Ta 2014 .

Yanzu Kusan shekaru Takwas Kenan Rabon Da Aganta a Fim Jaruma Zainab Idris Sai Muce Dake Allah Ya Baki Zaman Lafiya Da Mijinki Abass Sani Sadiq.

The post Hotuna: Tarihin Tsohuwar Jarumar Kannywood Zainab Idris appeared first on Labarai.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

Average rating 0 / 5. Vote count: 0

No votes so far! Be the first to rate this post.

As you found this post useful...

Follow us on social media!

We are sorry that this post was not useful for you!

Let us improve this post!

Tell us how we can improve this post?