Tue. May 21st, 2024
(Last Updated On: )

An haifi fitacciyar ‘yar Kannywood, marigayiya Saratu Gidado da ake yi wa lakabi da Daso, a ranar 17 ga watan Janairu 1968, a birnin Kano.
 
Saratu Gidado ta yi makarantun firamare da sankandare a birnin Kano sannan kuma ta halarci kwalejin fasaha ta Kaduna wato Kaduna Polytechnic, inda ta samu shaidar kammala babbar Diploma.
Daso
Jarumar ta shiga masana’antar fina-finan Kannywood ne a shekarar 2000, inda ta fara fitowa a wani fim mai suna Linzami da Wuta.
Daso lokacin tana matashiya
Kafin dai rasuwarta, jarumar ta sha tattaunawa da BBC, inda a ciki take bujuro da bayanai daban-daban da masu kaunarta ke son ji dangane da ita kuma za mu yi tsakure.
‘Ina yin fim saboda mijina wayayye ne’
Saratu Gidado Daso
‘Ina yin fim saboda mijina wayayye ne’, kalamai ne da marigayiya Saratu Gidado ta yi yayin wata tattaunawa da ta yi da BBC Hausa a shekarar 2019.
 
“Mijina ya bar ni na ringa fitowa a fina-finan Hausa duk da ina da aure saboda mijina wayayye ne kuma mai ilimi. Sannan kuma a ina cikin harkar fim muka hadu da shi saboda haka bai hana ni ba.
Daso lokacin tana yarinya
Ya fahimci cewa ina da damar da zan yi aikin da nake so idan dai har zan kare mutumcina na ‘ya Musulma kamar yadda duk wata mace ke aikin asibiti ko aikin jarida ko aikin koyarwa. Muna kiyaye mutumcin aurenmu da na iyalina” In ji Saratu.
Daso lokacin da take jaririya
Dangane kuma da yadda mai gidan nata yake ji a ransa idan ya ga tana wasan kwaikwayon, sai marigayiyar ta ce “ba ya jin komai tunda ya riga ya fahimci ba gaske ba ne. Ya san kwaikwayo ne. Ba ya jin komai.”
Daso tare da Lawan Ahmad lokacin daukar wani fim
‘Ni ba muguwa ba ce kamar yadda nake fitowa a fim’
Saratu Gidado lokacin tana jaririya
Marigayiya Saratu Gidado ta bayyana wa BBC cewa an fi ba ta damar taka rawa a zuwan ‘muguwa’, kasancewar ta iya taka rawar sosai.
 
“An fi ba ni damar taka rawar mai mugunta. Kuma mu mun san duk wani loko na mugunta amma fa a fim..hahahaha…Zan iya taka kowace irin rawa amma dai na fi jin dadin wannan din. Amma kowacce aka ba ni zan yi”. In ji Daso.
 
To sai dai ta kara da cewa “amma fa a rayuwa ta hakika ba haka nake ba. Ni ba mamugunciya ba ce. Ni mai kirkir ce a zahiri. Karewa ma ni ba na magana sosai.”
 
Bayan kwashekaru 18 a masana’antar fina-finan, sai marigayiyar ta yanke shawarar daina taka rawa ta fadace-fadace da guje-guje.
 
“yanzu gaskiya na koma taka rawar girma. Yanzu ba zan yi guje-gujen nan ba ko kuma na yi ta masifa saboda a kullum mutum girma yake yi.
 
‘Babbar baiwar da Allah ya yi min’
 
A shirin BBC Hausa na …Daga Bakin Mai Ita inda muke kawo jaruman fina-finan Kannywood, marigayiya Saratu Gidado ta shaida wa BBC cewa sirrinta da ba kowa ya sani ba a rayuwa shi ne “akwai baiwar da Allah ya yi min shi ne dan dai na yi wa mutum addu’a to insha Allahu kuwa za ta karbu.”
 
To sai dai dangane da darasin da marigayiyar ta koya a rayuwa shi ne butulci.
 
“Darasi babba da na koya a wurin jama’a shi ne sai ka yi wa mutum halacci amma shi kuma ya yi maka butulci. Amma da ma ni don Allah nake yi wa mutane alkairi saboda haka idan ma sun yi butulcin to don kansu.”
 
Wasu daga fina-finan da Daso ta yi
Kawo yanzu dai da wuya a iya hakkake yawan fina-finan da marigayiyar ta yi kasancewar ba ta raye ballanta ta tabbatar da hakan.
 
Sai dai kuma wasu fina-finan da suka fi yin fice nata sun hada da:

Nagari
Gidauniya
Mashi
Sarauniya
Daham
Alaqa
Fil’azal
Labarina
Sansani
Mazan fama
Gidan Iko
Cudanya
‘Yar Maiganye

 
 
Kafin rasuwarta kuma tana taka muhimmiyar rawa a wani fim mai dogon zango da bai fito ba tukunna mai suna Umarni.
 
Abin da ‘yan Kannywood ke faɗa kan Daso
Tun bayan da Saratu Gidado ta rasu a ranar Talata, abokan aikinta a masana’antar ta Kannywood da sauran al’umma ke ta fadin irin kyawawan halayen maragayiyar.
 
ga kadan daga cikin wasu da BBC ta samu tattaunawa da su:
 
Abba Al-Mustapha – “Mun yi babban rashin jajirtacciyar tauraruwa. Allah ya gafarta mata.
 
Baballe Hayatu – “Babu abin da za mu ce sai Innalillahi wa Inna Ilaihirraji’un. Mun yi rashin baiwar Allah mai barkwanci. Allah ya gafarta mata.”
 
Sahabi na kwana Casa’in – “Lallai wannan ba karamin rashi ba ne. Allah ya gafarta mata.”
 
Alhassan Kwalli – ” Ku san kamfanin na Sarauniya shi ne sillar janyo Daso cikin masana’anta. Muna zama lafiya. Mace ce mai son barkwanci. Muna fatan Allah ya karbi shahadarta.”
 
The post Cikakken Tarihin Marigayiya Saratu Gidado (Dawo) appeared first on Labarai.

How useful was this post?

Click on a star to rate it!

Average rating 0 / 5. Vote count: 0

No votes so far! Be the first to rate this post.

As you found this post useful...

Follow us on social media!

We are sorry that this post was not useful for you!

Let us improve this post!

Tell us how we can improve this post?